1 Peter 3

Matan Aure da Mazan Aure

1Haka ma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, domin in waɗansunsu ba su gaskata maganar ba, wataƙila a shawo kansu ba tare da magana ba 2saʼad da suka ga rayuwarku mai tsabta da kuma na ladabi. 3Kyanku bai kamata yǎ zama na adon jiki ba, kamar kitso da sa kayan ado na zinariya da kuma sa kaya masu tsada. 4Maimakon haka, kyanku ya kamata yǎ zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawaliʼu da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah. 5Gama haka matan masu tsarki na dā waɗanda suka sa begensu ga Allah suka yi wa kansu ado. Sun yi wa mazansu biyayya, 6kamar Saratu, wadda ta yi biyayya ga Ibrahim, har ta kira shi maigidanta. Ku ʼyaʼyanta ne mata in kun aikata abin da yake daidai, ba ku kuma ba tsoro dama ba.

7Mazan aure, ku ma, ku yi zaman sanin ya kamata yayinda kuke zama da matanku, ku girmama su a matsayin abokan zama marasa ƙarfi da kuma a matsayin magādan kyautar rai na alheri tare da ku, don kada wani abu yǎ hana adduʼoʼinku.

Shan Wahala Saboda Yin Ayyuka Alheri

8A ƙarshe, dukanku ku zauna lafiya da juna; ku zama masu juyayi, kuna ƙaunar juna kamar ʼyanʼuwa, ku zama masu tausayi da kuma tawaliʼu. 9Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi, sai dai ku sa albarka, gama ga wannan ne aka kira ku, ku kuma gāji albarka. 10Gama,

“Duk wanda yake so yǎ ji daɗin rayuwa,
yǎ kuma ga kwanaki masu kyau
dole yǎ kame harshensa daga mugunta
leɓunansa kuma daga maganar yaudara.
11Dole yǎ juye daga mugunta, ya aikata nagarta;
dole yǎ nemi salama yǎ kuma bi ta.
12Gama idanun Ubangiji suna a kan masu adalci
kunnuwansa kuma suna jin adduʼarsu,
amma fuskar Ubangiji tana gāba da masu mugunta.”
Zab 34.12-16

13Wa zai yi muku lahani in kun himmantu ga yin nagarta? 14Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.”
Ish 8.12
15Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawaliʼu da ladabi, 16tare da lamiri mai kyau, saboda waɗanda suke maganganun banza a kan kyawawan ayyukanku cikin Kiristi su ji kunya da irin ɓata suna da suke yi. 17Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta. 18Gama Kiristi ya mutu domin zunubi sau ɗaya tak, mai adalci saboda marasa adalci, don yǎ kawo ku ga Allah. An kashe shi a cikin jiki, amma an rayar da shi a Ruhu, 19ta wurin wanda kuma ya tafi ya yi wa ruhohin da suke a kurkuku waʼazi 20waɗanda dā ba su yi biyayya ba saʼad da Allah ya jira da haƙuri a kwanaki Nuhu yayinda ake sassaƙa jirgi. A cikinsa mutane kima ne kawai, su takwas, aka kuɓutar ta ruwa, 21ruwan nan kuwa kwatancin baftisma ne da yanzu ya cece ku ku ma-ba kawar da dauda daga jiki ba, sai dai yin alkawari na lamiri mai kyau ga Allah. Ya cece ku ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu, 22wanda ya tafi sama, yana kuma a hannun dama na Allah-malaʼiku, mulkoki da kuma masu iko suna masa biyayya.

Copyright information for HauSRK